Hukumar 'yan sandan Paris ta ba da bayyani kan shafinta na yanar gizo cewa, 'yan sanda za su dauki matakan hana zirga-zirgar motoci a wasu hanyoyi dake kewaye filin jirgin saman Charles-de-Gaulle da Orly, da hanyoyin mota dake kewaye ko cikin birnin na Paris, don ba da tabbaci ga tsaron shugabanni mahalarta taron da za su isa wuri yadda ya kamata.
Ma'aikatar harkokin wajen kasar Faransa ta ba da labari a ran 25 ga wata cewa, ya zuwa yanzu, shugabannin kasashe ko kusoshin gwamnatoci daban-daban 147 sun tabbatar da halartarsu a taron na Paris. (Amina)