Adadin farko da aka fitar game da hare-haren da aka kai a birnin Paris ya nuna cewa mutane 129 suka mutu yayin da wasu 352 suka jikkata a sakamakon lamarin.
Mai daukaka kara na birnin Paris Francois Morin ya shedawa manema labaru a ran 14 ga wata cewa, 'yan ta'adda 7 suka mutu, kuma 'yan sanda sun harbi 3 daga cikinsu a samemen da suka kai a gidan kallo da raye raye na Bataclan. Ban da haka, 'yan sanda sun gano wani fasfo na kasar Sham a gefen gawar wani dan kunar bakin wake da ya mutu a wajen filin wasa na Faransa.
Mista Morin ya ce, an tabbatar da cewa, wani dan kasar Faransa da aka haife shi a shekarar 1985 a karkarar birnin Paris yana da hannu da harin da aka kai a gidan kallo da raye-raye na Bataclan. Masu bincike na ganin cewa, akwai yiyuwar wasu da suka aikata laifi sun gudu zuwa kasar Belgium, hakan ya sa masu daukaka kara na kasar Faransa sun mika roko ga gwamnatin Belgium da ta ba su taimako.
A sabili da haka, firaministan kasar Belgium Charles Michel ya shedawa manema labaru a ran 14 ga wata cewa, 'yan sandan kasar sun gudanar da sammame sau da dama a Brussels hedkwatar kasar, inda suka cafke mutane 4 da ake tuhumarsu da hannu a hare-haren Paris, kuma daya daga cikinsu yana Paris a daren ran 13 ga wata, lokacin da hare haren suka faru. (Amina)