A yayin zaman, shugaba François Hollande na kasar Faransa ya yi wani jawabi, inda ya ce, ranar 13 ga watan Nuwamba rana ce da ba za su manta da ita ba har abada. A wancan rana, an dauki mugun matakin kai hare-hare kan birnin Paris. A cikin wadannan hare-haren da aka shirya a ketare, wasu masu laifin kisan gilla sun hallaka 'yan uwansu 130 tare da wasu daruruwa suka jikkata. Ya ce, dukkan 'yan Faransa suna makokin wadanda aka hallaka.
A yayin zaman makokin, a kan wani babban na'urar bidiyo, an nuna hotunan wadanda aka hallaka su a cikin harin daki daki.
Kafofin talibijin na kasar Faransa da wasu muhimman kafofin talibijin na kasa da kasa sun yada labaru game da zaman makokin kai tsaye. Mutane kimanin dubu 2, ciki har da firaministan gwamnatin Faransa da shugabannin majalisun dokokin kasar da ministocin gwamnati da wakilan jam'iyyun siyasa da sojojin rundunar ko ta kwana da wasu likitoci da nas-nas da dukkan iyalan wadanda suka mutu ko suka jikkata cikin harin sun halarci makokin. (Sanusi Chen)