A daya hannun kuma hakan ya sanya gurbataccen hazon, wanda ake samu sakamakon yawan fitar da hayaki mai gurbata muhalli, ya sake zamowa wani batun dake janyo hankalin jama'ar kasashen duniya.
Yadda gurbataccen hazo ya far wa kasashen Turai, ya tunasar da cewa, aikin daidaita matsalar samun gurbataccen hazo, wani aiki ne mai matukar wuya, wanda zai dauki lokaci mai tsawo kafin a cimma nasarar sa. Kaza lika kasashen Turai sun fara kayyade fitar da gurbatacciyar iska a farkon shekarun 1970, matakin da ya hada da kara inganta makamashi. Wadannan matakai sun yi amfani, amma ba a cimma nasarar kau da matsalar fitar da gurbatacciyar iska a kasashen Turai gaba daya ba tukuna. Yadda a wannan karo aka sake samun gurbataccen hazo a kasashen Turai ya nuna cewa, matsalar gurbataccen hazo ba a wata kasa ko wani yanki kadai ta takaita ba, wato matsalar da ta shafi dukkanin kasashe, tana kuma bukatar hadin gwiwar dukkanin kasashen duniya wajen warware ta. (Bello Wang)