Sakamakon haka, gamayyar kasa da kasa sun yi allah wadai da kakkausar harshe kan hare-haren da aka kai a Paris.
A ranar jumma'a 13 ga wata, babban magatakardan MDD Ban Ki-moon ya fidda wata sanarwa, inda ya yi allah wadai da harin ta'addanci na birnin Paris.
Shi ma Shugaban kasar Amurka Barack Obama ya bayyana daga fadar white house cewa , harin ta'addancin da aka kai ba kawai zai kasance harin ta'addanci da aka kai ga birnin Paris da kuma al'ummomin kasar Faransa bane, har ma ya kasance harin ta'addanci da aka kai ga dukkanin bil Adama na kasashen duniya, don haka yayi allah wadai da harin da kakkausar murya,tare da cewa, kasar Amurka za ta yi hadin gwiwa da jama'ar kasar Faransa da kuma kasa da kasa domin gurfanar da wadanda suka aikata wadannan laifuffuka gaban kuliya da kuma yaki da 'yan ta'adda da masu tsatsauran ra'ayi.
Haka shi ma, sakataren labarai na shugaban kasar Rasha Dmitri Peskov ya bayyana cewa, shugaban kasar Vladimir Putin ya nuna juyayi ga shugaban kasar Faransa da kuma al'ummomin kasar, inda ya bayyana goyon bayansa ga kasar wajen yaki da 'yan ta'adda da sannan kuma ya tausaya ma jama'ar kasa,tare da bayyana cewa, kasar Rasha za ta ba da taimako yadda ya kamata domin yin bincike kan harin. (Maryam)