A nashi bangaren, ministan harkokin cikin gidan kasar Faransa, mista Bernard Cazeneuve ya fada cewar, an tsara kan harin ne a kasashen waje, yayin da wasu mutanen dake cikin kasar ta Faransa suka tallafawa shirin. A halin yanzu, 'yan sandan kasashen Faransa da Belgium dake bincike kan musabbabin faruwar lamarin, suna kara samun ci gaba. 'Yan sandan kasar Faransa sun gabatar da wata sanarwa a ranar Lahadin nan, inda ake kira ga jama'a da su taimaka wajen yunkurin neman Abdeslam Salah, wanda ake zarginsa da hannu a harin na Paris, kafin haka kuma 'yan sandan Belgium ne suka sanar da cigiyar tasa.
A nasu bangare, masu kula da aikin shigar da kararraki na birnin Paris, sun tabbatar da cewa, Ismail Omar Mustafa wanda aka haifa a kasar Faransa a shekarar 1985, na daga cikin mutanen da ake zargi da hannu a kai harin, kuma a halin da ake ciki, tuni 'yan sanda sun tsare mutane 7 daga cikin dangin sa.
Ban da haka kuma, akwai labarin da ya nuna cewa, wasu mutane 3 daga cikin masu kai hare-haren a Paris sun kasance 'yan uwan juna. Cikinsu daya ya mutu, dayan ma an kama shi a Belgium, yayin da na 3 har yanzu ba a san inda yake ba.(Bello Wang)