in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Mummunar harin ta'addanci ya hallaka mutane kusan 200 a birnin Paris
2015-11-14 11:20:13 cri

Watanni bayan da aka kai harin ta'addanci a watan Janairu a birnin Paris na kasar Faransa wanda ya yi sanadiyar mutuwar mutane da dama sannan wassu suka jikkata, birnin ya sake fadawa cikin wani tashin hankalin harin ta'addancin a daren Jumma'an nan sakamakon jerin harbe-harbe da tashin bama bama a wurare da dama wanda ya hallaka mutane kusan dari 2, wadansu da dama kuma sun jikkata.

Rahotannin daga birnin Paris sun bayyana cewa an samu kashi kusan 7 daban daban na jerin harbe-harbe a tsakiyar birnin a wannan dare wanda daya ma ya koma harin yin garkuwa da mutane a zauren kallo da raye raye na Bataclan inda daruruwan jama'a suka yi cincinrindo domin kallon wasan wadansu kungiyar mawaka.

A lokacin da jami'an tsaron suka nemi kubutar da jama'a an yi arangama da ya yi sanadiyar mutuwar mutane fiye da 100 sannan cikin wadanda suka kai harin an hallaka guda 4.

Har ila yau an samu fashewar bama bamai guda biyu a kusa da babban filin wasanni na kasar wato Stade de France inda ake wasa tsakanin kungiyar kwallon kafa na kasar Jamus da Faransa kuma a wannan lokacin Shugaban kasar na Faransa Francois Hollande yana cikin 'yan kallo.

Sai dai ba'a bar 'yan kallo ko daya ya fito da filin wasan ba har sai da aka gama duk da fargaban da kowa ya fada game da abin da ke faruwa a cikin gari sannan kuma jiragen saukar ungulu na jami'an tsaro ya ci gaba da shawagi a sararin filin wasan. Bayan da ya samu barin filin wasan na Stade de France ya isa ma'aikatar harkokin cikin gida nan take Shugaba Hollande ya soki wannan hari da kakkausar murya yana mai bayyana shi da harin ta'addancin da bai da dalili.

A gunduma ta 11 ta birnin Paris, bayan harbe-harben da ya faru a zauren kallo na bayan aukuwar harin na zauren kallon Batacla, 'yan sanda sun tabbatar da cewa an yi garkuwa da mutane, kuma lokacin da suka isa wajen mutane 2 zuwa 3 masu dauke da manyan makamai suka bude musu wuta, in ji rahoton da gidan talabijin din kasar ya ruwaito.

Wani ganau wanda ya buga labarin a shafin yanar gizo na Europe1, Julien Pierce dan jarida ya ce mutane 2 zuwa 3 da ba su rufe fuskokinsu ba suka shiga zauren kallon dauke da bindiga kirar Kalachnikov kuma nan take suka fara harbi ta ko ina a kan jama'a.

A cikin wata 'yar gajeruwar sanarwa ta kafar talabijin, Shugaban kasar Faransan Francois Hollande ya sanar da kafa dokar ta baci da kuma umurnin rufe dukkan iyakoki a duk fadin kasar. Yana mai bayanin cewa za'a rufe wadansu wurare sannan za'a hana zirga zirgan ababen hawa a wadansu wurare tare da aiwatar da bincike a duk fadin kasar, sannan ya ce an zuba sojoji kusan 1,500 domin kara tabbatar da ba'a iya kai wani harin ba.

A sanarwar da mahukuntar birnin Paris ta fitar ta yanar gizo an bukaci kowa da ya zauna gida sannan kuma an dakatar da zirga zirgan jiragen kasa da motocin bas a gundumomi 10 da 11 na birni inda harin ya auku.

Zauren birnin na Paris ya tabbatar da cewa mutane 197 aka hallaka a daren wannan Jumma'an lokacin harbe harben da fashewar bama baman sannan kuma aka sanar da cewa za'a rufe dukkan makarantu da jami'o'i a ranar Asabar din nan.

Sai dai har yanzu ba'a samu wani kungiya da ta dauki alhakin wannan harin ba amma a rahoton da gidan talabijin din kasar ya ruwaito 'yan ta'addan sun kururuwan cewa '' domin Syria ne.''

Wannan harin ya biyo bayan harin da Faransa wadda take cikin kasashen da Amurka ke jagoranta domin dakile ayyukan kungiyar IS a kasashen Syria da Iraqi suka kai hari a kan wadansu muhimman wurare dake hannun kungiyar a wannan makon.

Faransa dai tana cikin shirin ko ta kwana a kan harin 'yan ta'adda, gwamnatin kasar ta kara azama a kan dakile ta'addanci iya matuka tare da kara adadin jami'an tsaro a duk fadin kasar domin sa ido a wuraren da ke da yuwuwar fuskantar harin.

Shugaba Hollande wanda ya soke aniyar shi ta halartar taron G20, zai jagoranci taron a kan tsaro a safiyar Asabar din nan bayan da mummunar harin ya girgiza tsarin tsaron kasar baki daya gabannin babban taro na kasa da kasa a kan sauyin yanayi da za'a yi a karshen watan nan.

A cewar ma'aikatar harkokin wajen kasar, filayen saukan jiragen sama da tashohin jiragen kasa za'a bude su kuma za'a cigaba da aiki a wajen, ya zuwa yanzu dai ba'a samu tabbacin adadin wadanda suka mutu ba a hukumance. (Fatimah Jibril)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China