A yau ne a nan birnin Beijing aka bude wata tashar talabijin da ke watsa shirye-shirye a fannin zirga-zirga da ta kasance ta farko a kasar Sin. Gidan rediyon kasar Sin CRI tare da hadin gwiwar hukumar zirga-zirga ta ma'aikatar tsaron jama'a ta kasar Sin ne suka kafa tashar wadda ke amfani da fasahar zamani.
Manufar kafa wannan tasha ita ce, samar da labarai da muhimman bayyanai a fannin zirga-zirga a hukunce, ba da shawara game da harkokin zirga-zirga don jin dadin rayuwar jama'a. Bugu da kari tashar na fatan zama wani muhimmin dandali a fannin zirga-zirga dake iya samar da hidima ga sassa da yawa a wannan fanni. (Amina)