Za a yi wannan gasa ce daga ranar 10 ga watan Yuni zuwa ranar 30 ga watan Satumba na shekarar da muke ciki. Sannan dukkan masu sauraronmu da masu karanta shafukan harsuna 65 na CRI da wadanda suke tafiyar da harkokin da suka shafi jin dadin jama'a za su iya shiga wannan gasa. Ana iya tsara talla game da batutuwan da suka shafi al'adun kasar Sin, kiyaye muhalli, kawo zaman lafiya a duniya, cimma burin Sinawa, nuna da'a da ladabi, game da rukunin mutane na musamman, da batun yawon shakatawa da neman bunkasuwar fasahohin kimiyya da makamatansu.
Gidan rediyon CRI zai tallafawa tallace-tallacen da suka yi fice, kuma za a nuna su a kafofin watsa labaru cikin harsuna 65 da CRI ke amfani da su. (Sanusi Chen)