Mr Ella ya bayyana kyakkyawar fata ga kafuwar wannan sashin,yana mai cewa, a watan Satumba na shekarar bara, an gabatar da shirye-shiryen telabiji na harshen Hausa na farko mai suna "Soyayyar matasan Beijing" a Nijeriya, matakin da ya bayyana cewa, Sinawa na mutunta jama'ar kasar da al'adunta.
Mr Ella wanda ya wakilci jakadan kasar Nijeriya a kasar Sin Malam Aminu Wali,yayi fatan kasashen biyu zasu kara mu'ammala a wannan fanni ta yin amfani da sashin yadda ya kamata. (Amina)