Shugaba Plevnelie ya bayyana cewa, CRI ta yi amfani da harsuna guda 65 wajen watsa labaran kasar Sin, gabatar da nasarorin da kasar Sin ta samu wajen raya kasa da kuma burinta, wannan aiki na da muhimmiyar ma'ana ga duk duniya. Ya kuma kara da cewa, jama'ar kasar Bulgaria sun mai da hankali da kuma nuna yabo ga sabon shirin gwamnatin kasar Sin wajen raya kasa, kasar Bulgaria tana son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin don tallafa wa al'ummomin kasashen biyu da kuma kiyaye zaman lafiya da zaman karko na kasa da kasa. (Maryam)