A jawabinsa na maraba da bakin, mataimakin shugaban gidan radiyon na CRI mista Xia Jixuan, ya ce CRI na samun ci gaba wajen yada labarai da shirye-shiryensa ga al'ummun nahiyar Afirka.
Mr. Xia, ya kara da cewa CRI na fatan karin hadin gwiwa tare da kafofin watsa labaru na kasashen Afirka, musamman ma a fannonin musayar shirye-shirye da ma'aikata, da fassarar fina-finai, da raya kafofin watsa labarai na zamani da dai sauransu. Duka da nufin karfafa huldar hadin gwiwa dake tsakanin Sin da Afirka a fannin watsa labarai, da kuma burin kara dankon zumunci tsakanin bangarorin 2. (Bello Wang)