in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Shugaban CRI ya gana da tsohon shugaban kasar Croatia
2013-12-19 19:37:05 cri

Shugaban gidan rediyon kasar Sin mista Wang Gengnian ya gana da tsohon shugaban kasar Croatia Stjepan Mesic a ranar Alhamis 19 ga wata a nan birnin Beijing. Yayin ganawar, mista Wang Gengnian ya ce gidan rediyon CRI kasancewarsa gidan rediyon kasar Sin daya tak dake watsa labarai da harshen Croatia, yana son ba da gudunmawa don kara azama ga hadin gwiwar dake tsakanin kasar Sin da kasar Croatia da ma sauran kasashen dake tsakiya da gabashin nahiyar Turai.

A nasa bangaren, mista Mesic ya ce, ya yi hira da wakilan CRI har sau 3. A cewarsa, samun fahimta tsakanin kasashe daban daban shi ne tushen hadin kai a tsakaninsu, kana kafofin watsa labaru na taka muhimmiyar rawa a fannin kara fahimtar juna tsakanin kasashen. Ya ce ya gamsu sosai da yadda ake watsa labarai da harshen Croatia a kasar Sin. (Bello Wang)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China