in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasashen Sin da Afirka sun amince su kafa ingantaccen tsarin kiwon lafiya na jama'a a kasashen Afirka
2015-10-07 14:49:51 cri

Ministocin harkokin lafiya na kasashen Sin da Afirka sun jaddada muhimmancin samar da tsarin kiwon lafiya mai inganci a nahiyar Afirka, musamman cibiyar yaki da hana yaduwar cututtuka a kasashen na Afirka har ma da kungiyar tarayyar Afirka ta AU.

Jami'an sun bayyana hakan ne yayin taron dandalin ministocin lafiya na kasashen Sin da Afirka karo na 2 da ya gudana a birnin Cape Town na kasar Afirka ta kudu.

A yayin taron mai take, "inganta matakan samar da kayayyakin kiwon lafiya a Afirka, inganta hadin gwiwar kasashin Sin da Afirka a bangaren kiwon lafiya na jama'a bayan barkewar cutar Ebola", bangarorin biyu sun amince sun kara bunkasa hadin gwiwa a bangaren matakan kula da lafiya na kasa.

Mahalarta taron sun kuma amince su kara inganta hadin kai a bangaren kula da lafiya ta hanyar bullo da matakan kula da lafiya masu inganci da kara karfafa hadin gwiwar musayar bayanai kan batutuwan da suka shafi harkokin kiwon lafiya sakamakon irin darussan da aka koya daga bala'in cutar Ebola.

A nata bangaren kasar Sin ta yi alkawarin cewa,za ta samar da guraben karo ilimi tare da horas da ma'aikatan kiwon lafiya na Afirka, a cikin kasashen na Afirka da kuma kasar Sin, yayin da su kuma kasashen Afirka za su rika tallafawa shirin samar da horon da kuma gano tare da horas da ma'aikatan da suka dace.

Daga cikin abubuwan da aka tsara a lokacin ganawar, kasar Sin za ta ci gaba da samar da kayayyakin aiki a cibiyoyin lafiyan da ta gina a kasashen Afirka ta yadda za su tafi da zamani. Bugu da kari, kasar Sin za ta ci gaba da tura ma'aikatan lafiya da za su rika yin aiki a kasashen Afirka, baya ga karin ma'aikatan lafiya 1,500 da za ta dauka cikin shekaru 3 masu zuwa. (Ibrahim)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China