A yayin wani zaman taro kan yaki da cutar Ebola a Afirka wanda aka kammala a ran 21 ga wata, Mr. Mwencha ya bayyana cewa, kasar Sin ta samar da taimako matuka ga gina cibiyar shawo kan cututtuka ta Afirka a fannonin ba da horo ga ma'aikatanta, koyar musu fasahohin tafiyar da ayyuka da kuma samar mata da kudade. Bugu da kari, ya kuma nuna godiya sosai ga kasar Sin kan taimakon da ta samar wa kasashen da suka yi fama da cutar Ebola kan hanyoyin yaki da cutar da kuma sake gina wadannan kasashe. (Maryam)