in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
AU ta yi kiran kasashen Afrika da su karfafa karfin bangaren kiwon lafiya
2015-07-22 10:56:25 cri

Ya kamata kasashen Afrika su kara rubanya kokarinsu domin tattara arziki da gaggauta zuba jari, ta yadda za a karfafa karfin bangaren kiwon lafiya, in ji manyan jami'an kungiyar tarayyar Afrika (AU) a ranar Talata.

Dole mu gaggauta zuba jari domin kafa al'ummomi masu juriya da tsare tsaren kiwon lafiya masu inganci da kwarewa dake zuwa daidai da kiwon lafiyar jama'a, da ba da jinya na farko, in ji shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe, da ke kuma shugaban kungiyar AU a wannon karo, a yayin wani zaman taron kungiyar kan yaki da cutar Ebola.

Ya kamata mu bunkasa tsare tsare, karfi da dabaru na samar da kudaden da suka dace domin fuskantar annobar cututtuka a nan gaba da kuma amsa bukatun gaggawa na jin kai, in ji mista Mugabe tare da jaddada cewa, babban burin shi ne na daukar matakan sake farfadowa bayan Ebola domin tabbatar da dawowar kiwon lafiyar jama'a.

Daga bakin ranar 14 ga watan Yuli, jimillar adadin masu dauke da kwayoyin cutar Ebola da aka rijista ya kai 27.679, wanda kuma cikin aka samu mutuwar mutane 11.276. Yawancin mace macen sun faru ne a yankunan da cibiyoyin kiwon lafiya da ba su da karfin ceto rayukan mutane, a cewar kungiyar AU.

Mataimakin kwamitin kungiyar AU, mista Erastus Mwencha ya bayyana cewa, wannan annoba, da ta yi yaduwar da ba a taba ganin irinta ba a yanmmacin Afrika, ana dangantaka ta da raunin tsare tsaren kiwon lafiya, da kuma rashin matakin da ya dace na fuskantar wannan annobar. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China