Cikin jawabin da ta gabatar a yayin taron, Madam Liu Yandong ta ce kasar Sin na dora muhimmancin gaske game da hana yaduwar sabuwar annoba, kuma ta tashi tsaye don shiga aikin hana yaduwar annoba a duniya.
Ta ce lokacin da cutar Ebola ta barke a yammacin Afrika a bara, Sin ta tura tawagar kiwon lafiya mafi girma a tarihin kasar zuwa wurin da annobar ta barke, tawagar da ta kasance wani babban ginshiki wajen yaki da cutar a duniya.
Har wa yau, tun daga rabin karnin da ya wuce, Sin ta tura likitoci kimanin dubu 23 zuwa kasashe ko yankuna 66, kuma jami'an lafiyar ta sun bada jiyya ga marasa lafiya miliyan 270. Kaza lika tawagar likitocin kasar ta yi hadin gwiwa da mazauna wuraren da ta gudanar da ayyuka, inda ta samu matukar goyon baya da karbuwa daga jama'ar kasashen da suka ci gajiyar tallafin.
Madam Liu ta ce, Sin da Amurka na da moriya kusan irin daya a fannonin kiwon lafiya, da yaki da annoba, kuma sun sauke nauyin dake wuyansu. Inda aka sanya batun kiwon lafiya cikin shawarwarin kasashen biyu ta fuskar musayar al'adu, wanda hakan ke kara ingiza hadin gwiwar kasashen biyu, tare da cusa sabbin abubuwa cikin mu'amalar bangarorin biyu. (Bako)