in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kasar Sin za ta horas da 'yan Ghana dabarun kiwon lafiyar mata
2015-09-09 10:51:44 cri
Kimanin ma'aikatan jiyya 22 'yan kasar Ghana ne za su taso daga Accra babban birnin kasar a Talatar nan domin halartar shirin bada horo kan dabarun kula da lafiyar mata a birnin Chengdu, wanda shi ne hedkwatar lardin Sichuan da ke kudu maso yammacin kasar Sin.

Shirin wanda zai kwashe kwanaki 90, zai maida hankali ne wajen horas da jami'an kiwon lafiyar Ghanan dabarun inganta sha'anin kula da lafiyar mata wanda zai gudana daga ranar 11 ga watan Satumba zuwa 9 ga watan Disambar wanana shekara.

Taron bitar yana karkashin shirin musayar jami'an kiwon lafiya na kasa da kasa ne a sashen kiwon lafiya na lardin Sichuan karkashin shugabancin sashen tsara iyalin na wannan lardi.

Da yake jawabi a bikin liyafar ban kwana da aka shiryawa mahalarta bitar, jakadan kasar Sin a Ghana Sun Baohong, ya ce Sin da Ghana sun shafe shekaru masu yawa suna cin moriyar juna a huldar kiwon lafiya, sannan ya jaddada cewar kasar Sin a shirye take wajen cigaba da karfafa wannan dangantaka.

A nasa jawabin, babban daraktan ma'aikatar lafiya na kasar Ghana Sylvester Anemana ya ce, kasar Sin ta dade tana tallafawa kasar Ghana musamman kan dabarun inganta sha'anin kula da lafiyar mata da kananan yara.

Ka zalika ya gargadi mahalarta bitar da su maida hankali wajen koyon dabarun kasar Sin na sha'anin kiwon lafiya domin samun ilmi wanda zai taimakawa kasar Ghana wajen magance matsalar mace macen mata masu juna da kananan yara.

Daga shekarar 2003 zuwa yau, sama da jami'an kasar Ghana 3,500 ne suka samu halartar kwasa-kwasai a fannoni sama da 20 a kasar Sin.(Ahmad)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China