Mataimakiyar firaministan kasar Sin Liu Yandong ta gana da babbar darektar hukumar kiwon lafiya ta duniya (WHO) Margaret Chan Fung Fu-chun a jiya Alhamis a birnin Geneva, kuma ta yi shawarwari tare da jakadun kasashen Guinea da Liberiya da Saliyo da kuma wakilin kungiyar tarayyar kasashen Afrika dake birnin Geneva.
Madam Liu Yandong ta ce, kasar Sin tana son karfafa aikin kiwon lafiya a duniya tare da kungiyar WHO bayan da aka kusan kawo karshen cutar Ebola. Kasar Sin za ta shiga aikin kafa tsarin rigakafin ciwace-ciwace da manyan ayyukan more rayuwar jama'a na kiwon lafiya na kasashen Afrika bisa bukatun kasashen Afrika da amincewarsu, domin taimaka musu wajen kara karfin tinkarar al'amuran kiwon lafiya na ba zata.
A nata bangare, Margaret Chan Fung Fu-chun ta ce, kungiyar WHO ta nuna yabo ga gudunmawar da kasar Sin ta bayar wajen yaki da cutar Ebola a kasashen Afrika. Gwamnatin Sin ta riga ta kafa tsari mai amfani na tinkarar batutuwan kiwon lafiya cikin gaggawa, tana fatan kungiyar za ta karfafa hadin gwiwa tare da kasar Sin da yada kyakkyawan fasahohin da kasar ta samu.
Ban da haka kuma, jakadun kasashen Afrika sun bayyana cewa, a lokacin da kasashen yammacin Afrika ke fama da cutar Ebola, kasar Sin ce ta ba da taimakon farko, hakan ya burge mutanen Afrika sosai. Sun yi imani da cewa, kasar Sin za ta ci gaba da ba da taimako ga kasashen Afrika.(Lami)