Madam Li ta bayyana a lokacin da ya ke jawabi a bikin bude taron ministocin Sin da Afrika karo na biyu kan hadin gwiwa ta fuskar kiwon lafiya da aka yi a wannan rana cewa, Madam Tu ta gano sabuwar hanyar ce bisa nazarin da ta yi kan fasahar maganin gargajiya na kasar Sin, maganin da aka samar dangane da ci gaban da Madam Tu ta samu ya zama magani mafi kyau a duniya wajen magance zazzabin cizon sauro.
A yayin wannan taro, kasashen Sin da kasar Comores dake gabashin Afrika sun yi takaitaccen bayyani kan aikin da suka yi cikin hadin gwiwa wajen kawar da zazzabin cizon sauro ta hanyar sabon sakamakon da Madam Tu ta samu, an ce, wannan sakamako ya taimaka wajen rage yawan mutanen da suke mutuwa sakamakon zazzabin cizon sauro zuwa sifiri cikin shekaru 8 da suka gabata, tare kuma da rage yawan mutanen da suka kamu da cutar da kashi 98 cikin dari. A cewar Madam Li, wannan taro zai gabatar da ayyuka da dama da Sin da kasashen Afrika za su yi tare don yaki da zazzabin cizon sauro. (Amina)