Shirye-shirye sun yi nisa, game da kafa babbar cibiyar yaki da cututtuka ta kasashe mambobin kungiyar raya yammacin Afirka mai helkwata a tarayyar Najeriya.
Hakan a cewar wata sanarwa da ma'aikatar lafiyar Najeriyar ta fitar, ya biyo bayan amincewar da mahukuntan kasar suka yi da a kafa cibiyar a kasar, da kuma irin muhimmiyar rawa da Najeriyar ta taka a fannin yaki da cutar Ebola.
Sanarwar ta kara da cewa, cibiyar yaki da cututtukan ko CDC a takaice, za ta ba da gudummawa wajen ganin an cimma burin inganta harkokin kiwon lafiya a yankin na yammacin Afirka. Kaza lika ana sa ran wannan cibiya za ta zamo wani makami na tunkarar kalubalen lafiya a yammacin Afirka, musamman ta hanyar tallafin da za ta rika samu daga kungiyar AU, da ma sauran sassan masu ruwa da tsaki.
Karkashin wannan muhimmin tsari, zababbun cibiyoyin bincike dake sassan yammacin Afirka, za su rika gudanar da hadin gwiwa wajen nazari a sabuwar cibiyar ta CDC da za a kaddamar a Najeriya.
A wani ci gaban kuma, ma'aikatar lafiyar Najeriyar ta ce, za ta goyi bayan wani yunkuri, na kafuwar babbar cibiyar binciken harkokin lafiya ko ACDC, wadda za ta kunshi daukacin nahiyar Afirka baki daya. (Saminu)