Ministan ma'aikatar kudin kasar Sin Lou Jiwei, ya ce, tattalin arzikin kasar Sin ya shiga wani sabon matsayi na inganci, domin a yanzu haka ana hasashen karuwarsa da kaso 7 ciki dari nan da shakeru 4 zuwa 5 masu zuwa.
Mr. Lou ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa, bayan kammalar taron yini biyu, na gwamnonin bankunan kasashe mambobin kungiyar G20, wanda ya gudana a birnin Ankara dake kasar Turkiya.
Da yake jaddada wannan batu, gwamnan babban bankin al'ummar kasar Sin Zhou Xiaochuan, ya ce, babu wani dalili da zai sanya a ci gaba da rage darajar kudin kasar Sin RMB. Ya ce, yanzu haka ribar hannayen jarin kasar na samun tagomashi gabanin watan Yunin wannan shekara. A gabar da kasuwar hannun jarin ta birnin Shanghai ta daga da kaso 70 cikin dari, tsakanin watan Maris zuwa Yuni.
Mr. Zhou ya kara da cewa, Sin ta aiwatar da manufar warware matsalolin dake fuskantar kasuwar hannayen jari har karo 3, ciki hadda matakin da aka dauka cikin watan Agusta wanda ya shafi sassan duniya baki daya.
A daya hannun kuma, kasar ta Sin na daukar karin matakan dakile fuskantar karyewar tattalin arziki na tsahon lokaci, matakin da kuma ya yi matukar tasiri wajen baiwa kasuwar hannayen jarin kasar kariya.
Ministan ma'aikatar kudin kasar Sin Lou Jiwei ya kuma bayyana cewa, ko shakka babu, tattalin arzikin kasar na cikin yanayi mai cike da tabbas. Ya ce, a baya an dauki matakan tabbatar da karuwar tattalin arzikin kasar da kaso 9 zuwa 10 cikin dari, irin wadannan matakai kuma za su kare tattalin arzikin, ta yadda zai kai ga tsayawa kan hasashen karuwarsa da kaso 7 cikin dari nan da shekaru 5 masu zuwa.
Bugu da kari Mr. Lou ya bayyana cewa, shekaru 5 masu zuwa za su zamo masu wuya, sakamakon matakan gyare-gyare da ake dauka, gabanin cimma nasarar da ake fata nan da shekarar 2020.
Kari kan dalilan hasashen nasarar ci gaban shi ne, tattalin arzikin kasar ta Sin zai fi ba da karfi a fannin kasuwar cikin gida maimakon ta waje, da ma jarin da kasar ke zubawa a ketare.
Daga nan sai ya jaddada aniyar mahukuntan kasar na ci gaba da aiwatar da karin manufofi, wadanda za su baiwa babban bankin kasar damar kara yawan kudaden da yake kashewa, ya zuwa kaso 10 cikin dari, sama da kaso 7 bisa dari dake cikin kunshin kasafinsa. (Saminu)