in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Taron tattara kudade don neman samun bunkasuwa na MDD ya mai da hankali sosai kan tattalin arzikin Afrika
2015-07-16 10:24:28 cri

Kungiyar tarayyar kasashen Afrika (AU) da ma'aikatar kudi ta kasar Habasha sun kira taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin Afrika a jiya Laraba a birnin Addis Ababa, inda suka mai da hankali sosai kan bunkasuwar masana'antu da aikin gona na Afrika, inda jama'a suka yi kira ga kasashen Afrika da su ci gaba da raya manyan ayyukan more zaman rayuwa a nahiyar.

An kira taron dandalin tattaunawa kan tattalin arzikin Afrika ne a gyefen taron tattara kudade don neman samu bunkasuwa na kasa da kasa na MDD karo na 3.

Shugaban bankin raya Afrika Donald Kaberuka ya bayyana a gun taron cewa, raya manyan ayyukan more zaman rayuwa zai taimaka ga bunkasuwar Afrika. A cikin shekaru 10 da suka gabata, bankin raya Afrika ya zuba jarin da yawansu ya kai dalar Amurka biliyan 28 a bangaren raya manyan ayyukan more zaman rayuwa a Afrika, wanda ya ninka sau uku idan aka kwantanta da daukacin kudaden da bankin ya bayar a cikin shekaru 40 da suka gabata. Ya kuma jaddada cewa, muddin ba a inganta muhimman ayyukan more zaman rayuwa a Afrika ba, wannan na iya taka birki ga bunkasuwar tattalin arzikin nahiyar.

Bugu da kari, mahalartan taron sun jaddada cewa, dole ne kasashen Afrika su kara zuba jari da gaggauta bunkasa manyan ayyukan more zaman rayuwa da raya ayyukan makamashi na bola-jari, a kokarin cimma burin da ake da shi na raya masana'antu da aikin gona na zamani.(Lami)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China