Duk da wahalhalun tattalin arziki da ake fuskanta, kasar Afrika ta Kudu ba za ta canza hasashenta na cimma kashi 5 bisa dari na karuwar tattalin arzikinta ba nan da shekara ta 2019, in ji shugaba Jacob Zuma a jiya Laraba.
Shugaba Zuma a wajen wata muhawara a kan kasafin kudin fadar shugaban kasar da aka yi gaban majalissar dokokin kasar, ya ce, za'a kara nace wa wannan kuduri saboda daukacin al'ummar kasar dole ne su yi aiki tare, su kuma ba da nasu gudunmuwa don cimma wannan burin.
Mr Zuma dai ya tsai da wannan bukata ne a jawabinsa ga daukacin al'ummar kasa a watan Fabrairu.
Ya bayyana wa 'yan majalissun cewa, an kara jaddada wannan burin ne da sanin cewa ba abu ne da zai zo da sauki ba wajen cimma shi.
A rahoton shi na watannin uku-uku da ya fitar ranar Talata, kididdigar kasar ta Afrika ta Kudun ta ce, ma'aunin GDP ya yi kasa a watanni uku na farko na wannan shekarar, inda ya karu kawai da kashi 1.3 bisa dari idan aka kwatanta da kashi 4.1 bisa dari na watanni 3 na karshen shakarar 2014. (Fatimah)