Ofishin hukumar MDD mai lura da tattalin arzikin nahiyar Afirka ko UNECA a takaice, ya fidda wani sabon rahoto game da yanayin da tattalin arzikin nahiyar ke ciki a wannan shekara ta bana.
Hukumar ta UNECA ta fidda wannan rahoto ne a ranar Laraba a birnin Kigali, fadar mulkin kasar Ruwanda. Rahoton ya ce ko da yake tattalin arzikin Afrika ya samu bunkasuwa cikin sauri a cikin shekaru 10 da suka gabata, a daya hannun kuma yana fuskantar rashin samar da isassun guraben ayyukan yi.
Rahoton ya kara da cewa duba da saurin karuwar yawan al'ummar nahiyar, yawan karuwar guraben ayyuka da ake samu a Afrika bai wuce kaso 2.9 cikin dari kacal ba, matakin dake nuni ga matukar karancin guraben ayyuka dake addabar kasashen nahiyar.
Kaza lika rahoton ya yi kira ga kasashe daban daban dake nahiyar Afirka da su kara ingiza cinikayya gaba, domin raya masana'antu, da habaka kasuwanni.
Bugu da kari rahoton ya ce, dole ne kasashen Afrika su gyara tsarin tattalin arzikin su, ta yadda za su iya amfana daga albarkatun kwadago masu dimbin yawa wajen samar da kayayyaki, a maimakon fitar da albarkatun su zuwa kasashen ketare. (Lami)