Wakilin kamfanin Ignatius Ong Ming Choy ne ya bayyana hakan yayin taron manema labarai yau a nan birnin Beijing, inda ya ce a halin yanzu, bayanan da ke hannun fasinjojin suna daidai da bayanan wadanda suka sayi tikitn jirgin daga Kuala Lumpur zuwa birnin Beijing.
Jirgin saman kasar ta Malaysia dai ya bace ne a ranar Asabar da misalin karfe 1 da minti 20 na dare a lokacin da yake ratsa yankin Ho Chi Minh na kasar Vietman dauke da fasinjoji 227, kuma 154 daga cikinsu Sinawa ne da kuma ma'aikatan jirgin 'yan kasar Malaysia 12. (Ibrahim)