in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Jirgin saman Sin ya gano wasu abubuwa da ake zaton na jirgin saman da ya bace
2014-03-24 15:26:56 cri

Ma'aikatan jirgin saman kasar Sin samfurin IL-76 sun gano a ranar Litinin wasu abubuwan da ake zaton na jirgin saman kasar Malaisiya MH370 da ya bace ne a kudancin ruwan tekun Indiya, a yayin wani aikin bincike.

Ma'aikatan jirgin kasar Sin sun aiko da sakamakonsu da ya shafi kewayen digiri mita 95,11 zuwa gabashi da digiri mita 42, 54 zuwa kudanci ga cibiyar gudanar da bincike ta kasar Australiya, kuma jirgin ruwan fasa kankara Xuelong na kasar Sin yana kan hanyar zuwa wannan yanki.

Wani wakilin kamfanin dillancin labarai na Xinhua dake kan wannan jirgin sama ya bayyana cewa, masu bincike sun gano wasu abubuwa biyu bisa ruwa masu girman gaske, da kuma wasu abubuwa farare kankana masu yawa a tarwatse bisa fadin kilomita da dama.

Haka kuma wakilin na Xinhua, ya kara da cewa, ganin cewa jiragen ruwan bincike na kasar Sin za su koma sansaninsu, ma'aikatan sun bukaci bangaren kasar Australiya da ya tura wasu jiragen sama a wannan wuri domin kara zurfafa bincike. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China