in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Sin za tana kokarin shirya wata gasar Olympics na yanayin sanyi mai kyau
2015-08-22 18:24:55 cri
Shugaban kasar Sin Xi Jinping ya gana da shugaban kwamitin gasar wasannin Olympics na kasa da kasa Thomas Bach a filin wasan motsa jiki na kasar a yau asabar inda ya bayyana cewa, gwamnatin kasar Sin za ta cika duk alkawurran da ta yi wajen shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na yanayin sanyi ta shekarar 2022, don ya zama wani gaggarumi a duniya.

A nasa bayanin Mr. Thomas Bach ya taya birnin Beijing murnar samun bakuncin gudanar da gasar wasannin motsa jiki ta Olympics na yanayin sanyi na shekarar 2022, yana mai cewa, gwamnatin kasar Sin ta yi kokarin neman bakuncin gasar da kyakkawan niyya, goyon baya ne da ta nuna wa harkokin Olympics na kasa da kasa da kuma kwamitin gasar wasannin Olympics din.

Ya ce, kwamitin ya goyi bayan gwamnatin kasar Sin wajen ciyar da aikin motsa jiki a kasar gaba don haka yana da imani cewa, babu shakka, kasar Sin za ta shirya gasa mai kyau, kuma yana son yin hadin gwiwa da kasar Sin kan wannan aiki. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China