in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Yang Jiechi ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 69
2015-08-02 13:33:58 cri
Jiya Asabar 1 ga wata, wakilin majalisar gudanarwar kasar Sin Yang Jiechi ya gana da shugaban babban taron MDD karo na 69, kana ministan harkokin wajen kasar Uganda Sam Kahamba a nan birnin Beijing.

A yayin ganawar tasu, Yang Jiechi ya bayyana cewa, shekarar bana ita ce cikon shekaru 70 na kafuwar MDD da na cimma nasarar yakin Fascist na duniya, kasar Sin na fatan gamayyar kasa da kasa za su yi hadin gwiwa domin samun sakamako masu gamsuwa cikin jerin tarukan koli da MDD za ta yi a watan Satumba, kiyaye zaman lafiyar kasa da kasa da kuma inganta ci gaban kasa da kasa.

Haka kuma, Mr. Kahamba ya taya wa kasar Sin murnar cimma nasarar samun damar karbar bakuncin wasannin Olympic na yanayin sanyi na shekarar 2022, ya kuma nuna godiya ga kasar Sin kan goyon bayan da ta samar wa ayyukan MDD.

Mr. Kahamba ya ce, MDD na son yin hadin gwiwa tare da kasar Sin wajen tsara shirin neman bunkasuwa bayan shekarar 2015 da kuma fuskantar sauyin yanayin duniya yadda ya kamata. (Maryam)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China