Mambar ofishin siyasa na kwamitin tsakiya na JKS,kuma mataimakiyar firaministan kasar Madam Liu Yandong wadda ta jagoranci tawagar neman bakuncin wasannin Olympic na yanayin sanyi na shekarar 2022 ta dawo nan birnin Beijing da yammacin jiya Lahadi, inda ta samu tarba daga bangarori daban-daban.
A cikin jawabinta a filin saukar jiragen sama, Madam Liu ta ce tawagar ta cimma nasara a Kuala Lumpur, wanda ya gamsar da JKS da jama'ar kasar Sin. Ban da haka kuma, a cewarta wasikar da shugaban kasar Sin Xi Jinping ya mika mata ta fatan alheri ga nasarar da aka samu a Kuala Lumpur, da fatan cimma nasarar shirya wasannin, ta karfafa mata gwiwa.
Ta ce ya kamata a ci gaba da kokari na cika alkawarin da Sin take yi don bude wani sabon shafi a tarihin Olympic.
Dadin dadawa, direktan birnin Beijing Mr. Guo Jinlong ya yi jawabi a wannan rana, inda ya bayyana kyakkyawan fata da gaisuwa ga dukannin mambobin tawagar, tare da nuna godiya ga duk wadanda suka yi kokarin ba da gudunmawa wajen neman daukar bakuncin gasar a wannan karo.
Yayin bikin maraba da aka yi a filin saukar jiragen sama, tawagar wakilan yara sun mikawa tawagar furari tare da gabatar da kyalen rubutun kalamai dake cewa, "Maraba da dawowa tawagar dake samun nasara", wanda ya bayyana farin cikin dukkan Sinawa.
Kwamitin wasannin Olympic na duniya ya sanar a ran 31 ga watan Yuni cewa, birnin Beijing ya sami damar karbar bakuncin wasannin Olympic na shekarar 2022. A kuma gudanar da wannan babbar gasa ta wasanni daban-daban ne bayan ko wane shekaru 4. (Amina)