Tawagar kasar Sin mai kula da aikin neman karbar bakuncin gasar Olympics ta lokacin sanyi a shekarar 2022, ta isa birnin Lausannen na kasar Switzerland, domin halartar taron musayar ra'ayi, tsakanin birane masu neman karbar bakuncin gasar, da kuma mambobin kwamitin Olympics na duniya, taron na yini 2 da ya fara daga Talata.
Mataimakiyar firaministar kasar Sin Liu Yandong, ita ce ta jagoranci tawagar kasar Sin, wadda kuma ta kunshi manyan jami'ai da suka hada da shugaban hukumar wasanni ta kasar Liu Peng, da magajin garin birnin Beijing, kuma shugaban kwamitin neman karbar bakuncin gasar Wang Anshun.
Wannan ne dai karo na karshe da za a gudanar da taron musayar ra'ayi tsakanin bangarorin masu ruwa da tsaki, gabanin cikakken zama na 128, na kwamitin Olympics na duniya dake tafe a ranar 31 ga watan Yuli mai zuwa.
Tuni dai kwamitin binciken biranen da ke neman karbar bakuncin gasar ta Olympics ya gabatar da rahoton binciken sa ga babban kwamitin IOC, inda cikin sa ya jinjinawa karfin da biranen Beijing da kuma Zhangjiakou suke da shi, wajen karbar bakuncin gasar ta shekarar 2022, tare da yabawa birnin Beijing, game da aniyar sa ta sake amfani da gine-ginen da aka yi amfani da su yayin gasar Olympics ta shekarar 2008. (Lami)