Jaridar "I' équipe" wadda ke yada labarun wasannin motsa jiki ta fitar da wani dogon bayani mai take "dalilai mafi karfi", inda ta nazarta dalilan da suka sa birnin Beijing ya samu nasara. A cikin bayanin, an bayyana cewa, "da samun kuri'u 44 ne birnin Beijin ya bude wani sabon shafin tarihi", wato, ba ma kawai ya taba shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta yanayin zafi ba, har ma ya zama birnin da zai shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta yanayin hunturu."
Sannan a kan jaridar "I'équipe", an kuma wallafa wani bayani daban, inda ake fatan birnin Paris da a fili ne ya ce zai nemi samun izinin shirya gasar wasannin motsa jiki ta Olympic ta yanayin zafi ta shekarar 2024 don haka dole ya koyi da yadda birnin Beijing ya samu nasara. A cikin bayanin, an ce, "ko shakka babu karfin tattalin arzikin birnin Beijing ya kasance wani muhimmin dalili, amma ba dukka dalilai ba." Wannan bayani ya ruwaito maganar da Mr. Tony Estanguet ya yi, cewar "wani shirin dake kunshe da kome da kome ya fi muhimmanci, alal misali, hangen nesa, dimbin abubuwan Olympics da za a iya gada a nan gaba, matsayin 'yan wasannin motsa jiki da amfaninsu, da kuma matakan yada tasirin Olympic cikin dogon lokaci a nan gaba da dai makamatansu." (Sanusi Chen)