Ranar 28 ga watan Yulin shekarar 2014 da muke ciki, rana ce ta tunawa da cika shekaru dari da barkewar yakin duniya na farko. A wannan rana kasashen duniya da yawa sun shirya bukukuwan tunawa da wannan lamari.
Kamfanin dillancin labarun AFP na kasar Faransa, ya bayyana cewa, dakin nune-nune na mutanen da suka rasa rayukansu, sakamakon kisan kare dangi da aka yi musu a kasar Serbia, ya shirya wani baje koli na takardun yakin duniyar na farko a ranar 28 ga wata, ciki hadda takardu masu yawa da a karon farko aka fitar da su ga jama'a.
A matsayinsa na fadar gwamnatin kasar Serbia yayin yakin duniyar na farko, birnin Nis da ke kudancin kasar ya shirya bikin bude duwatsun tunawa da yakin a wannan rana. Kafin hakan an shirya wani biki a daren ranar Lahadi 27 ga wata, a tsohuwar fadar Kalemegdan da ke tsakiyar babban birnin kasar Belgrade.
Ministan kwadago na kasar ya bayyana a gun bikin cewa, dalilan shirya bikin su hada da tunawa da sojojin kasar da suka rasu a yakin, da ma amfani da wannan biki wajen yin kira, ga dorewar zaman lafiya ga daukacin al'ummar kasar da zuriyata.
A nasa tsokaci kuwa, shugaban kasar Austria Heinz Fischer, ya yi kira ga kasashen duniya da su koyi darasi daga abin tarihin da ya faru. Fischer wanda ya bayyana hakan yayin bikin bude harkokin al'adu a birnin salzburg, ya kara da cewa kamata ya yi a lura cewa yaki ba zai iya warware matsaloli ba, kuma dole ne a yi kokarin wanzar da yanayin zaman lafiya, wanda a cewarsa ya zama wajibi a yi kokarin nemansa ta hanyoyin da suka dace. (Danladi)