Hakan a cewar hukumar ya bakanta ran kasar ta Sin, inda Sin din ta nuna rashin amincewa ga matsayin na kasar Japan wanda ke kunshe cikin sabuwar takardar bayanin aikin tsaro da gwamnatin Japan din ta gabatar.
Kaza lika kasar Sin ta tsaya tsayin daka kan manufar bin hanyar samun bunkasuwa cikin lumana, da manufofin kiyaye tsaron yankunan ta, da kara karfafa tsaron ta, da raya aikin soja wanda ke karkashin hakkin hukumomin ta, a matsayin ta na kasa mai mulkin kai, kana babu wata kasa ko yanki dake da ikon tsoma baki cikin wannan hakki na Sin.
Tuni dai kasar Japan ta bayyana matsayarta ta ci gaba da samun bunkasuwa cikin lumana, tare da gudanar da manufar kare kai kawai, a sa'i daya kuma, tana fatan amfani da sabuwar dokar kiyaye tsaro, don gyara manufofin aikin soja, da fara gudanar da aikin soja don taimakawa kasashen dake kawance da ita ta fuskar ayyukan soji ko shiga fagen daga.
Wannan manufa ta kasar Japan ta shaida cewa, tana raba kafa a fannin manufofin harkokin waje, wadanda zasu kawo illa ga zaman lafiya a yankin nahiyar Asiya da tekun Pasifik. (Zainab)