in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin ya yi jawabi kan batun Japan
2014-11-23 17:00:28 cri
A jiya Asabar 22 ga wata ne, kakakin ma'aikatar harkokin wajen Sin Hong Lei ya amsa tambayoyin manema labarai kan takardar mai da martani da gwamnatin Japan ta bayar.

Hong Lei ya bayyana cewa, tun asali tsibirin Diaoyu mallakar kasar Sin ne. Gwamnatin Sin tana tsayawa tsayin daka kan kiyaye ikon mallakar yankunanta. Kamata ya yi Japan ta daina duk wasu ayyukan da suka sabawa doka game da ikon mallakar yankun kasar Sin. Kuma Sin ta nuna rashin amincewa ga shugabannin Japan da su kai ziyara a haikalin Yasukuni ta kowace hanya, da fatan Japan za ta waiwayi tarihi game da harin da ta kai sauran kasashen duniya, tare da koyon darasi daga garesu.

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China