in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Amurka ta bukaci kasar Japan da ta yi kokarin warware matsalar tarihi ta hanyan yin shawarwari
2015-01-07 16:49:59 cri
Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka Jen Psaki ta bayyana a ranar Litinin cewa, kasar Amurka ta bukaci kasar Japan da ta ci gaba da yin kokarin warware matsalar da ta shafi tarihi tare da kasashe makwabtanta ta hanyar yin shawarwari.

Jen Psaki ta bayyana a gun taron manema labaru da ma'aikatar harkokin wajen kasar Amurka ta gudanar a wannan rana cewa, kasar Amurka ta mai da hankali kan jawabin da firaministan kasar Japan Shinzo Abe ya yi a wannan rana.

Bisa labarin da aka bayar, an ce, Shinzo Abe ya bayyana a gun taron manema labaru a Litinin cewa, zai bayyana yadda zai gaji ra'ayoyin tsofaffin ministocin kasar kan tarihi a cikin jawabin da zai gabatar a wannan shekara na cika shekaru 70 bayan kawo karshen yakin duniya na biyu, kana zai bayyana matsayinsa ga sauran kasashen duniya kan yadda za a bada gudummawa wajen tabbatar da zaman lafiya da na karko a yankin Asiya da tekun Pasific har ma a duniya baki daya. (Zainab)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China