A ranar 8 ga watan ne kwamitin kula da harkokin sadarwar ta hada-hadar kudi, ta bankin duniya ya fidda rahoton dake cewa, a watan Agustan bana, kudin Sin RMB ya wuce kudin Sweden, da na Koriya ta Kudu, da kudin kasar Rasha, har ya zama kudin da ke matsayi na 8 a duniya, da aka fi yin cinikayya da shi. Har wa yau rahoton yace yawan kudin Sin RMB da ake yin amfani da shi wajen cinikayya a duniya ya kai kashi 1.49 cikin 100.
Bisa kididdigar da wannan kwamiti ya fitar, an ce, a watan Janairun bara, RMB na matsayi na 11, kuma yawan kudin Sin RMB da aka yi amfani da shi wajen cinikayya a duniya ya kai kashi 0.92 cikin 100. Daga watan Janairu na shekarar 2012 zuwa watan Agustan bana kuwa, yawan cinikayyar da aka yi da kudin RMB ya karu da kashi 113 cikin 100.
Bisa nazarin da aka yi, an ce, kimanin kashi 60 cikin 100 na cinikayyar da ake yi da kudin Sin, an yi shi ne a Birtaniya. (Bako)