Furman ya bayyana hakan ne yayin jawabinsa a cibiyar "Brookings" dake birnin Washington, inda ya bayyana cewa darajar kudin Sin RMB ta karu da kashi 30 cikin dari tsakanin shekarar 2010 zuwa yanzu, kuma yawan rarar kudin da Sin ta samu bisa yawan GDPn kasar ya ragu, daga kaso 10 cikin dari a shekarar 2007, zuwa kaso 2.1 cikin dari a shekarar 2014.
Furman ya ce, kasar Amurka za ta ci gaba da sa kaimi ga kasar Sin, wajen cika alkawarin gudanar da kwaskwarima kan kasuwar kudin RMB. (Zainab)