A cikin sanarwar, an ce, za a daidaita darajar kudin Sin RMB bisa yanayin tattalin arzikin kasar. Game da tsarin kafa darajarsa, IMF ya ba da shawara ga kasar Sin da ta gaggauta nuna sassauci kan darajar RMB, wato nan da shekaru 2 ko 3 masu zuwa, za a cimma burin sauya darajar kudaden musaya bisa bukatun kasuwanni a kasar.
Game da makomar tattalin arzikin kasar, IMF ya ce, dalilin da ya sa, Sin ta sassauta don raya tattalin arziki, ganin yadda aka canja salon bunkasuwar tattalin arziki da take aiwatarwa cikin shekaru 10 da suka gabata na wani dogon lokaci.
Bisa hasashen da IMF ya yi, tattalin arzikin Sin zai samu karuwa da kashi 6.8 cikin 100 a bana, abin da ya yi daidai da yadda kasar Sin ta kiyasta, wato kashi 7 cikin 100.(Bako)