A jiya ne ofishin bankin duniya da ke nan kasar Sin ya sanar cewar shugaban bankin duniya Kim Jim-Yong zai kawo ziyarar aiki Sin daga ranar 15 zuwa 17 ga wata, da nufin inganta hadin gwiwa a tsakanin bankinsa da kasar Sin a fannin raya sha'anin hada-hadar kudi da bankin zuba jari kan muhimman ayyukan more rayuwa na Asiya da aka kafa ba da dadewa ba.
Shugaba Kim Jim-Yong ya kuma bayyana godiyarsa ga gwamnatin kasar Sin cikin wata sanarwar da ya fitar, musamman ma ma'aikatarta ta kudi, bisa dukufar ta kan aikin hadin gwiwa tare da bankin na duniya.
Haka kuma ya ce, bankin yana muna maraba da kasar Sin da ta kara taka rawarta a ayyukan ci gaban duniya. Sannan tana nuna godiya ga kasar Sin kan yadda take marawa bankin baya.
Bugu da kari, shugaban ya kara nuna farin cikin sa tare da nuna goyon ga kasar Sin kan manufofin na yin gyare-gyare, wadanda ya yi imani da cewa,za su kara kyautata dangantakar abokantaka a tsakaninsu, sannan za ta taimaka wajen samun dauwamammen ci gaban duniya da kowa da kowa zai amfana. (Kande Gao)