A shekarar bara ne dai kasar Sin ta zamo kasa mafi girma a fannin cinikayya tare da kasar Afirka ta Kudu cikin shekaru 6 a jere, kana kasar Afirka ta Kudu ta zamo ta farko wajen yawan cinikayya da kasar Sin a nahiyar Afirka.
A bana kuma, ana sa ran gudanar da taron ministoci karo na shida na dandalin tattaunawa kan hadin gwiwar Sin da Afirka a kasar Afirka ta Kudu, game da hadin gwiwar kasashen biyu a fannnin samar da kayayyaki, da gina ababen more rayuwa, wanda zai sa kaimi ga fadada cinikayya, ko zuba jari, ko tattara kudaden haraji ta hanyar kudin Sin RMB a nahiyar Afirka.
Kafuwar tsarin cinikayya ta hanyar kudin RMB a Afirka dai zai bunkasa hada-hada tsakanin masu halartar kasuwannin Afirka ta Kudu, da ma na dukkanin nahiyar Afirka dake gudanar da cinikayya da kudin na RMB. (Zainab)