in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Bankin duniya ya samar da dala miliyan 50 domin yaki da cututtuka a gabashin Afrika
2015-07-09 13:14:30 cri

Bankin duniya ya amince da ba da rancen kudi na dalar Amurka miliyan 50 domin yin rigakafi da binciken cututtuka a cikin tsare tsaren kiwon lafiya na kasashen da ke gabashin Afrika.

Mai ba da rancen ya bayyana cewa, wadannan kudade za su taimaka wajen karfafa samun wani tsarin dakunan bincike na kiwon lafiyar jama'a mai inganci, tare da ba da kwarin gwiwa ga karfin sanya ido kan cututtuka, rigakafi da shiryawa a kasashen Burundi, Kenya, Tanzaniya da kuma Uganda.

Haka kuma, rancen kudin zai taimaka wajen fadada aikin kiwon lafiya a wannan shiyya, ta hanyar kawo karin dakunan binkice a yankunan da ke kan iyakoki, in ji bankin duniya a cikin wata sanarwa a birnin Nairobi.

A cewar wannan sanarwa, kudaden da suka fito daga kungiyar ci gaban kasa da kasa za su dogaro bisa ayyukan shirin tsarin binciken kiwon lafiya na jama'a a gabashin Afrika da ke gudana domin kafa wani tsarin dakunan binciken kiwon lafiyar jama'a mai karfi, ta yadda za a iyar yin bincike da sanya ido kan cututtuka masu yaduwa.

Mamo Umuro, shugaban ayyukan binciken kiwon lafiyar jama'a na kasa, a ma'aikatar kiwon lafiya ta kasar Kenya, ya bayyana cewa, wannan shirin ya kara fitar da ayyukan dakunan bincike a fili, da bullo da wata hanya ta dogaro kan shaidu.

A cewar bankin duniya, domin tabbatar da cewa tsare tsaren kiwon lafiya sun kasance masu inganci, shirin zai mai da hankali kan kulawa da kwarewa kan cututtuka masu yaduwa, har ma da kafa wasu tashoshin killacewa, da kuma karfafa ayyukan sanya ido kan al'umma. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China