Mr.Koroma ya bayyana cewa, an kawar da dokar hana taruwar jama'ar kasa, a sa'i daya kuma, za a bude wuraren motsa jiki, wuraren nishadi na dare, sinima da kuma dakunan cin abinci da dai sauransu, haka kuma, za a sake bude manyan kasuwanni a kasar. Daga bisani kuma, Babura masu dauke da fasinja za su iya yin ayyukansu tsakanin karfe shida na safe har zuwa karfe sha biyu na dare. Duk da cewa dokar ta bacen za ta cigaba aiki a ranar a Lahadi.
A sa'i daya kuma, Mr.Koroma ya bayyana wa jama'ar kasa cewa, an sake dawo da cutar Ebola a kasar Liberia bayan kasar ta sanar da kawo karshen cutar ba da dadewa ba, lamarin da ya nuna cewa, akwai wuya da a iya kawo karshen cutar, ya kamata jama'ar kasar su mai da hankali kan wannan batu.
A ran 30 ga watan Yuli na shekarar da ta gabata, shugaba Koroma ya taba fidda wata sanarwa a fili, inda ya sanar da shigar kasar cikin halin dokar ta bace, a sa'i daya kuma, an fara yaki da cutar Ebola a duk fadin kasar. (Maryam)