Mr. Zhao wanda ya bayyana hakan yayin zantawar sa da ministan lafiyar kasar Abu Bakar Fofanah, ya kara da cewa wani jirgin saman kasar Sin dauke da nau'o'in rigunan kariya 100,000, ya bar Sin zuwa Saliyo a karshen makon nan. Ana kuma fatan karin kayan tallafin da Sin za ta gabatar a wannan karo, za su kara karfafa yakin da ake yi da yaduwar Ebola.
Har wa yau Mr. Zhao ya shaidawa ministan lafiyar kasar ta Saliyo cewa, tuni Sin ta fara tsara manufofin taimakawa kasar bayan shawo kan cutar, duba da cewa a halin da ake ciki, an fara ganin alamun nasarar dakile yaduwar Ebola a kasar.
Da yake maida jawabin Mr. Fofanah, ya jinjinawa kwazon kasar Sin bisa wannan tallafi, ya na mai cewa kasar Sin ce ta fara agazawa Saliyo, a yakin da ta sha fama da shi da cutar ta Ebola, tun ma kafin shugaba Ernest Koroma na Saliyon, ya gabatar da kokwan barar tallafin kasashen waje.
Mr. Fofanah ya ce Sin ta zamo kasa daya tilo da ke ci gaba da amsa kiran Saliyo game da samar da karin tallafin yaki da Ebola, a gabar da sauran kasashen duniya ke ja da baya. (Saminu)