in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ebola: Saliyo ta kaddamar da shirin neman mafita
2015-07-26 13:37:47 cri
Kasar Saliyo, daya daga cikin kasashen yammacin Afrika uku da annobar cutar Ebola ta daidaita, ta kafa wani shirin gyara da ke maida hankali sosai kan bangarorin da suka shafi kiwon lafiya, ilimi, noma da dangantakar jama'a. Annonar cutar Ebola, da har yanzu ba ta fita ba kwatakwata daga kasar Saliyo ba, ta janyo mammunar illa ga tattalin arzikin wannan kasa dake yammacin Afrika.

Shugaban kasar Saliyo yayi kiran gamayyar kasa da kasa da ta taimakawa kasarsa wajen yaki da cutar Ebola. A cewar shugaban Saliyo Ernest Bai Koroma, bisa yankuna goma sha hudu da kasar take da su, goma daga cikinsu ba a samu cutar Ebola ba tun fiye da kwanaki 90, haka su ma sauran yankunan uku basu samu sabbin wadanda suka kamu da cutar ba tun farkon shekara. (Maman Ada)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China