in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta shirya dandalin tattaunawar "Lanting"
2015-06-20 13:30:15 cri
A jiya Jumma'a 19 ga wata, ma'aikatar harkokin waje ta Sin ta shirya dandalin tattaunawa mai taken "Kulla sabuwar hulda tsakanin Sin da Amurka ta hanyar yin shawarwari da amincewa da juna da yin hadin gwiwa da juna" a dakin "Lanting" na ma'aikatar da ke nan birnin Beijing,

Dandalin da ya samu halartar mataimakin ministan harkokin wajen kasar Sin, Zheng Zeguang, da mataimakin ministan kudi na Sin Zhu Guangyao, da kuma mataimakin ministan ilmi Liu Limin wadanda duk suka gabatar da jawabai.

A cikin jawaban nasu sun yi bayani dangane da shawarwari karo na 7 da za a gudanar tsakanin Sin da Amurka bisa manyan tsare tsare a fannin tattalin arziki da kuma shawarwari karo na 6 tsakanin manyan jami'an Sin da na Amurka a fannin al'adun bil'adam.

An bada labarin cewa, za a gudanar da wadannan shawarwari biyu daga ranar 23 zuwa 24 ga wannan watan na Yunin a birnin Washington na Amurka inda a matsayin manzon musamman na shugaban kasar Sin Xi Jinping, mataimakiyar firaministan Sin Liu Yandong za ta jagoranci shawarwarin tsakanin manyan jami'an Sin da na Amurka a fannin al'adu tare da sakataren harkokin waje na Amurka John Kerry.

Shi kuma mataimakin firaministan Sin Wang Yang da mamban majalisar gudanarwa ta Sin Yang Jiechi za su jagoranci dayan shawarwarin tare da manzannin musamman na shugaban Amurka Barack Obama, sakataren harkokin wajen Amurka John Kerry da kuma ministan kudin Amurka Jacob J.Lew.

Wadannan shawarwarin biyu tsakanin Sin da Amurka na da ma'ana sosai wajen kara samun fahimta da amincewa da juna har ma da sa kaimi ga yin hadin gwiwa da mu'amala tsakaninsu a fannoni daban daban, da kuma share fagen ziyarar da shugaban kasar Sin Xi Jinping zai kai Amurka a watan Satumban dake tafe yadda ya kamata.(Fatima)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China