in Web hausa.cri.cn
ShigaZaman RayuwaAfirka a YauSin Ciki da WajeAmsoshin TambayoyiWasannin Motsa JikiChina ABC::: TSOHO :::
Za a mai da hankali kan sabbin fannoni a gun taron tattaunawa tsakanin manyan jami'an Sin da Amurka ta fuskar mu'amalar al'adu
2015-06-22 13:29:42 cri

Nan ba da dadewa ba za a gudanar da taron tattaunawa a tsakanin manyan jami'an kasashen Sin da Amurka dangane da yin mu'amalar al'adu karo na 6 a birnin Washington, hedkwatar kasar Amurka. Kristie Kenney, mai ba da taimako ga mataimakin sakataren harkokin wajen Amurka da ke kula da harkokin gabashin Asiya da tekun Pasific, ta shaidawa wakilinmu cewa, za a mai da hankali kan wasu sabbin fannoni a yayin taron tattaunawar. A kwana a tashi ana kara yin mu'amala a fannoni daban daban a yayin taron tattaunawar, inda bangarorin 2 suke kara yin mu'amala da juna yadda ya kamata, kana an samu karin hukumomi da suka halarci taron, lamarin da zai inganta mu'amala a tsakanin jama'ar Sin da Amurka.

Madam Kenney ta kara da cewa, Amurka na daukar taron tattaunawar da za a yi a bana da muhimmancin gske. A kuma sa ran shugaba Barack Hussein Obama na Amurka zai gana da madam Liu Yandong, mataimakiyar firaministan kasar Sin da kusoshin Sin da za su halarci taron a fadar gwamnatin Amurka ta White House.

Baya ga fannonin da Sin da Amurka suke hadin kai a baya kamar al'adu, ba da ilmi, kiwon lafiya, motsa jiki, a cewar madam Kenney, bangarorin 2 za su habaka wasu fannonin yin hadin gwiwa a bana, alal misali, yin hadin gwiwa a fannin kiwon lafiyar al'umma a duk fadin duniya, inganta kwarewar mata ta fuskar ba da jagoranci. (Tasallah Yuan)

Labarai masu Nasaba
Ra’ayoyinku
  Webradio
Saurare (GMT 11:30pm - 12:30pm)
Bayanai da Dumi-dumi
© China Radio International.CRI. All Rights Reserved.
16A Shijingshan Road, Beijing, China