Kakakin ma'aikatar harkokin wajen kasar Lu Kang ya shaidawa manema labarai cewa, babu kamshin gaskiya game da abin da Amurkan ke yayatawa.
Lu ya ce, duniya na sane da cewa, Amurka na satar bayanai ta fannoni dadan-danam kama daga siyasa, harkokin kasuwanci har ma da na daidaikun jama'a, kuma hakan ya sabawa dokokin kasa da kasa.
Don haka ya ja hankalin kasar ta Amurka da ta kwana da sanin cewa, akwai bukatar ta yi wa duniya bayani game da zargin da ake mata na satar bayanan jama'a, kafin ta zargi wasu da aikata irin wannan danyen aiki.
A farkon watan nan ne aka shiga rumbun adana muhimman bayanan ma'aikatan gwamnatin Amurka, inda santocin kasar da dama ke zargin Sin da aikatawa. (Ibrahim)