Kamfanin samar da wutar lantarki na kasar Sin ya sanar a ran 13 ga wata a nan birnin Beijing cewa, Sin ce ke kan gaba a duniya a fannin samar da wutar lantarki ta karfin iska, kana kamfanin na kan matsayin farko a duniya wanda ya samu bunkasuwa mafi sauri wajen samar da wutar lantarki ta karfin iska da hasken rana. Sin ta kwashe shekaru biyar da rabi wajen raya tsarin samar da wutar lantarki ta karfin iska, yayin da Amurka da Turai sun shafe shekaru 15 suna yin shi.
An ba da labari cewa, kamfanin ya dukufa kan aikin samar da wutar lantarki ta karfin iska da hasken rana, kuma hakan ya taimaka sosai wajen samun bunkasuwa a wannan fanni.
Ban da haka, kamfanin na kokarin raya tsarin samar da wutar lantarki da daga karfin rarraba makamashi masu daraja, kana ya sa kaimi ga samar da wutar lantarki ta karfin ruwa bisa sabon tsari na zamani. (Amina)