Jimillar kudin wannan aiki ta tashi zuwa kusan Sefa biliyan 80 kwatankwacin dalar Amurka miliyan 150, kuma wani kamfanin gine gine na kasar Sin na "Sino-Hydro" aka baiwa kwangilar gina wannan tasha da rabin kudaden suka fito daga kungiyoyin dake tallafawa kasar Nijar. Tashar za'a gina ta bisa fadin hekta 80 kuma aikin zai shafe tsawon watanni 20. A tsawon shekaru da dama, Niamey, babban birnin kasar Nijar da kuma sauran wasu kauyuka na kasar na fama da matsalar dauke wutar lantarki ta tsawon sa'o'i a cikin yini musamman a lokacin tsananin zafi. (Maman Ada)